Najeriya-Nijar

Nijar da Najeriya za su kulla yarjejeniyar yaki da safarar mutane

Wasu bakin haure da ke kokarin tsallakawa Turai.
Wasu bakin haure da ke kokarin tsallakawa Turai. AP - Mosa'ab Elshamy

Nijar da Najeriya, na shirin kulla wata yarjejeniya da za ta bai wa kasashensu damar shawo kan matsalar safarar bil’adama. Wanan ya biyo bayan wata ziyara da shugaban hukumar Yaki da safarar bil Adama a Najeriya NAPTIP ya kai tare da ganawa da takwaransa na Jamhuriyar Nijar. Ga rahoto Umar Sani daga Agadas