Amurka - Afirka

Amurka za ta soma jigilar alluran rigakafin Korona miliyan 25 zuwa Afirka

Ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines yayin aikin sauke allurar rigakafin Korona na kamfanin AstraZeneca / Oxford a karkashin shirin COVAX a Filin jirgin saman Bole dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Maris 7, 2021.
Ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines yayin aikin sauke allurar rigakafin Korona na kamfanin AstraZeneca / Oxford a karkashin shirin COVAX a Filin jirgin saman Bole dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Maris 7, 2021. REUTERS - TIKSA NEGERI

Amurka ta sanar da shirin jigilar alluran rigakafin cutar Korona miliyan 25 zuwa Afirka, shirin da ta ce zai fara ta kan kasashen Burkina Faso, Djibouti, da kuma Habasha.

Talla

Za a soma jigilar allurar rigakafin zuwa kasashen 3 ne nan da 'yan kwanaki, yayin da sauran kasashen nahiyar ta Afirka 49 za su karbi alluran na Johnson & Johnson, Moderna ko Pfizer cikin ‘yan makwanni masu zuwa.

Daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, kasashen Djibouti da Burkina Faso za su karbi alluran Johnson & Johnson dubu 151 da 200, yayin da Habasha za ta karbi allurai dubu 453 da 600.

Yanzu haka dai adadin mutanen da Korona ke kashewa a Afirka  ya karu da kashi 43 cikin 100 a cikin mako guda, matsalar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta danganta da rashin gadajen kwantar da marasa lafiya a sahin bada kulawa na musamman da kuma karancin tukwanen iskar oxygen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.