Masar

Masar ta sallami wasu masu rajin kare hakkin bil'adama da ke tsare

Wata 'yar jarida mai rajin kare hakkin bil'adama da hukumonin Masar suka sallama daga kurkuku.
Wata 'yar jarida mai rajin kare hakkin bil'adama da hukumonin Masar suka sallama daga kurkuku. Don EMMERT AFP/File

Gwamnatin Masar ta salami wasu masu rajin gwagwaryar kare hakkin bil'adama su shida, daga gidan kaso, ciki har da dan jarida Esraa Abdel-Fattah wanda ya yi fice yayin gwagwaryar shekara ta 2011.

Talla

Matakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kasar Amurka ta gargadi Masar game da take hakkin bil’adama.

Tun hawar Shugaban kasa Abdel-Fattah Alsisi karagar mulki  a shekarar 2014 yake tafiyar da mulkin tamkar na kama karya, kuma masana na ganin matakin yanzu na sallaman masu rajin kare jama’a na daga cikin matakan samun sa'ida daga uzurawar da kasashen duniya ke yiwa Masar din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.