Afirka ta Kudu

Zuma ya bayyana gaban kotu karon farko tun bayan tsare shi

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ranar 26 ga watan Mayun 2021.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ranar 26 ga watan Mayun 2021. PHILL MAGAKOE POOL/AFP/Archivos

Shari'ar cin hanci da rashawa da aka dade ana yi wa tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma da ke daure za ta ci gaba da gudana a wannan Litinin, duk da tashe-tashen hankulan da suka auku a sassan kasar bayan da aka daure shi saboda kin bin umarnin kotu.

Talla

Tsohon shugaba Zuma na fuskantar tuhume-tuhume 16 da suka shafi laifukan zamba, da almundahana yayin sayen jiragen yaki a shekarar 1999, jiragen yaki sojin sama da kananan jiragen ruwa na sintiri gami  da kayan wasu kayayyakin sojoji daga wasu kamfanonin Turai guda biyar lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Ana zargin Zuma da karbar cin hanci daga daya daga cikin kamfanonin mai suna Thales na kasar Faransa wanda tuni aka tuhume shi da rashawa da kuma halatta kudaden haram.

An dai fara yi wa Zuma shari’ar ce a watan Mayu bayan dage zamanta da aka yi a lokuta da dama, saboda lauyoyinsa da suka rika fafutukar don ganin an soke tuhumar.

Zuma mai shekaru 79 musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa, yayin da shi ma kamfanin saida makaman na Thales ya musanta zargin da ake masa.

Zanga-zangar magoya bayan Zuma ta rikide zuwa tashin hankalin da ya lakume rayukan mutane fiye da 200 ne ranar 29 ga watan Yuni a sassan Afrika ta Kudu bayan da aka sami tsohon shugaban da laifin raina babbar kotun kasar na kin bayyana kansa, abinda ya sa aka daure shi tsawon watanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.