Mali

Kiris ya rage a yi wa shugaban Mali kisan gilla a Masallaci

Shugaban rikwonkaryar Mali Kanar Assimi Goïta
Shugaban rikwonkaryar Mali Kanar Assimi Goïta © Annie Risemberg, AFP

Wasu mutane biyu sun yi yunkurin hallaka shugaban rikon kwaryar kasar Mali Kanar Assimi Goita ta hanyar amfani da wuka a daidai lokacin da ake gudanar da sallar idi a wani masallaci da ke birnin Bamako fadar gwamnatin kasar ta Mali.

Talla

Bayanai sun ce maharan su biyu ne, yayin da daya da ke dauke da wuka ya yi yunkirin afka wa shugaba Goita, to sai dai jami’an tsaron da ke kare shugaban suka murkushe shi, yayin da wasu bayanai ke cewa an ga jini a inda lamarin ya faru duk da cewa ba a san ko na waye ba ne.

Daga bisani, fadar shugaban kasar ta ce, shugaba Goita yana cikin koshin lafiya biyo bayan wannan yunkuri da aka kitsa da niyar hallaka shi.

Ministan Kula da Harkokin Addinai na kasar Mamadou Kone wanda ke cikin masallacin lokacin wannan hari, ya ce tuni aka kama wanda ya yi yunkurin kashe shugaban, kuma an kaddamar da bincike don gano wadanda ke da hannu a wannan lamari.

Shi dai kanar Assimi Goita, ya jagoranci sojoji don kwace ragamar mulkin kasar Mali ne daga hannun Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan shekarar bara, kafin daga bisani ya sake kwace mulki karo na biyu daga hannun shugaban rikon Bah Ndaw.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI