Uganda - Korona

Mutane sama da 800 sun karbi allurar rigakafin korona ta bogi a Uganda

Wani likita a kasar Uganda yayin karbar allurar rigakafin korona samfurin Oxford/AstraZeneca.
Wani likita a kasar Uganda yayin karbar allurar rigakafin korona samfurin Oxford/AstraZeneca. Badru KATUMBA AFP/File

Mutane sama da dari 8 aka yiwa allurar rigakafin korona ta bogi a kasar Uganda, a wata badakala da ake ganin akwai sanya hannun likitoci da ma’aikatan lafiya har ma da jami’an gwamnati.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa an yiwa mafi yawan mutanen ne allura da ruwa maimakon sinadarin dakile cutar koronan.

An bankado cewa an fara yiwa mutane wannan allura ta bogi ne a tsakanin watannin Mayu da Yuni, lokacin da kasar ke cikin tsananin fama da cutar ta korona da akalla yawan masu kamuwa dubu 1 da dari 7 kowacce rana.

Masu gudanar da wannan allura dai na karbar kudade a hannun wadanda ke son ayi musu cikin gaggawa, kuma cikin wadanda aka yiwa irin wannan allura akwai ma’aikatan gwamnati, da jigajigan ‘yan siyasa.

Shugaban kwamitin yaki da korona na kasar Dr Warren Naamara ya ce tuni aka kama jami’an lafiya da dama da hannu wajen aikata wannan badakala, a yayin da ake neman wasu manyan likitoci da aka gano suna da hannu kasancewar tuni suka tsere.

Tuni dai shugaban kasar Yuweri Museveni ya bada umarnin dakatar da yin alluran rigakafin korona a fadin kasar har sai an kammala gudanar da bincike, yana mai cewa wannan abin takaici ne, idan aka yi la’akari da yadda gwamnati ta samar da wadannan allurai a kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.