Burundi-Ma'aidinai

Burundi ta kori kamfanonin Turai saboda haraji

Wani yankin hakar ma'adinan karkashin kasa
Wani yankin hakar ma'adinan karkashin kasa AFP - MARTHE BOSUANDOLE

Hukumomin Burundi sun dakatar da ayyukan wasu manyan kamfanonin hakar ma’adanai na kasashen waje, bisa zargin su da kwange wajen biyan kudaden harajin.

Talla

A cewar gwamnatin kasar, baya ga kwange wajen biyan harajin, kamfanonin na kuma cutar gwamnatin wajen ba ta kason da ya dace bayan hako albarkatun karkashin kasar.

Cikin kamfanonin da aka dakatar, akwai Gakara Project guda daga cikin manyan kamfanonin hakar ma’adanai a duniya.

A wata wasika da Ministan Ma’adanai na kasar Ibrahim Uwizeye ya aike wa kamfanonin ya ce ya zama dole a dauki matakin, la’akari da yadda kamfanonin suka gwada halin zamba cikin aminci da kuma take yarjejeniya.

Kamfanonin da aka aika wa wasikar guda bakwai sun hada da na Burtaniya da na China da na Russia, kuma suna aikin hakar gwal da sinadarin Clotan da ake amfani da shi wajen hada kayayyakin laturoni.

Minista Ibrahim ya ce, kamfanonin sun kwashe tsawon shekaru suna cutar kasar da ma al’ummarta la’akari da yadda ake tsara kasafin kudin karkashin sanya ran samun kudade daga kamfanonin.

Yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka shafi kudi da dukiya na daya daga cikin manyan batutuwan da shugaban kasar Evariste Ndayishimiye ya sanya a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.