Tanzania

Jagoran adawar Tanzania zai fuskanci tuhumar ta'addanci a kotu

Freeman Mbowe, shugaban jam'iyyar adawa a Tanzania.
Freeman Mbowe, shugaban jam'iyyar adawa a Tanzania. RFI Kiswahli

Gwamnatin Tanzania  ta ce tana tsare da Jagoran babbar jam’iyyar adawar kasar bisa zargin da ake masa na ta’addanci, bayan kama shi yayin wani samame da suka kai, lamarin daya tada hankulan kasashen duniya.

Talla

An dai kama Freeman Mbowe da wasu mutane 15 ne kafin wayewar garin Laraba, a wata dirar mikiya dake tuni da irin mulkin kama karya da kasar ta fuskanta a karkashin mulkin marigayi tsohon shugabanta.

Gwamnatin kasar ta ce tana ci gaba da tsare Mbowe bisa zargin ta’addanci da ya kunshi kashe jam’ian gwamnatin kasar kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan sandan kasar David Misime ya bayyana a wata sanarwa, yana mai cewa sun gabatar da manyan shuwagabanin jamiyyu 6 a gaban kotu.

Jam'iyyar  adawa ta Chadema ta ce jam’ian sun gudanar da bincike a gidan Mbowe dake Dar es Salam tare da karbe masa nau’rar komfutansa  da na wasu daga cikin iyalansa kafin garzayawa da shi gidan kaso dake tsakiyar kasar.

'Yan sanda dai sun kama Mbowe ne da wasu jami’an a  birnin Lake Victoria Port  dake Mwanza a shirye-shiryen taron gangami da ke tafe nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.