Saliyo

Majalisar Saliyo ta amince da soke dokar hukuncn kisa

Wani dake gidan wakafi a kasar Saliyo
Wani dake gidan wakafi a kasar Saliyo Anne-Sophie FAIVRE LE CADRE AFP/File

'Yan majalisar Saliyo sun kada kuri'ar amincewa da soke hukuncin kisa, inda ta zama kasar Afirka ta baya-bayan nan da ta yunkuro don hana zartar da hukuncin kisa.

Talla

Mafi yawan 'yan majalisar sun kada kuri'ar amincewa da yin kwaskwarimar kawar da hukuncin kisan, a cewar wani dan jaridar AFP wanda ke cikin zauren majalisar.

Za a maye gurbin hukuncin kisa da ɗaurin rai da rai ko mafi ƙarancin shekaru ɗaurin kurkuku na shekaru 30 saboda laifuka kamar kisan kai ko tawaye.

Ba a taɓa aiwatar da kisa ba a ƙasar tun daga shekarar 1998, kuma sau da yawa ana canja hukuncin kisa.

Amma Saliyo, wacce har yanzu take murmurewa bayan yakin basasa na shekaru da dama, ta sha fuskantar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam saboda sanya hukuncin kisa a kundin tsarin Mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.