morocco - bakin haure

Sojin ruwar Morocco sun ceto bakin haure 368 a gabar ruwa

Sojojin Spain yayin tsamo bakin haure daga ruwa.
Sojojin Spain yayin tsamo bakin haure daga ruwa. Antonio Sempere AFP

Rundunar sojan ruwan Morocco ta ceto bakin haure 368 a makon da ya gabata ciki har da kananan yara uku yayin da suke kokarin tsallaka tekun Meditaraniya don isa kasar Spain.

Talla

Kamfanin dillacin labarai na MAP ya ruwaito cewa,  bakin hauren, galibinsu sun fito daga yankin kudu da Saharar Afirka, an ceto su ne tsakanin ranakun Talata zuwa Juma’a lokacin da kan kanan kwale-kwalen roba dake dauke da su suka shiga cikin matsala.

Ko a makon da ya gabata, rahotanni suka ce sojojin ruwan Morocco sun ceto bakin haure 344 a tekun Bahar Rum da Atlantic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.