Kamaru-Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun kashe dakarun Kamaru 7

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP

Mayakan Boko Haram sun ci karfin wani sansani soji a yankin arewa mai nisa na Jamhuriyar Kamaru, inda suka kashe sojoji 7 tare da raunata da dama, a cewar majiyoyi daga yankin.

Talla

Da misalin karfe 4 na yammacin Asabar din nan ne suka kai samame  sansanin sojin da ke garin Sagme, dauke da makamai a cikin ayarin motoci 6, wasunsu sanye da khakin yaki na sojoji.

Bayan an shafe sa’o’i ana gwabza fada ne aka kashe kwamandan sansanin da wasu abokan aikinsa 6.

Kungiyar Boko Haram da tsaginta na  ISWAP sun zafafa munanan hare-hare a kan jami’an tsaro da fararen hula a yankin arewa mai nisa na Kamaru  a cikin ‘yan shekarun nan; yankunan kan iyakar Najeriya da ke makwaftaka da Kamarun ma ba su tsira ba.

Sun kuma yawaita sace fararen hula, musamman mata da yara.

Yaki da mayakan Boko Haram da ISWAP ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu 36 tun da aka fara shi a shekarar 2009, kuman ya raba kusan mutane miliyan 2 da gidajensu.

A tsakiyar watan Yuni ne kungiyar Boko Haram ta tabbatar cewa an kashe shugabanta, Abubakar Shekau a wata arangama da kungiyar ISWAP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.