Afrika ta Tsakiya

Wata kungiyar agaji za ta dakatar da ayyukanta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kauyen Yade, dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kauyen Yade, dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. © REUTERS

Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers ta sanar da cewa za ta dakatar da ayyukanta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya  bayan da kungiyoyin da ke daukar makamai suka yawaita hare-hare a kan  ma’aikatanta.

Talla

Kungiyar ta zargi mayakan da kai hare-hare  a kan ma’aikata da ofisoshinta.

A watan Yuni, mayakan sun yi wa ayarin motocin kungiyar Medicins Sans Frontiers kwanton bauna a kan hanyarsa zuwa asibiti, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wata mai kula da mara lafiyar.

Gabanin harin watan Yunin, sai da wasu 'yan bindiga suka kashe ma'aikatan kungiyar Medicins Sans Frontiers 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.