Chadi

Sabon manzon Tarayyar Afirka na musamman a Chadi ya isa kasar

Basile Ikouébé,manzon Tarayyar Afirka na musamman a Chadi.
Basile Ikouébé,manzon Tarayyar Afirka na musamman a Chadi. AFP - MARY ALTAFFER

Manzon musamman da Kungiyar Tarayyar Afirka ta nada zuwa Chadi Basile Ikouébé  dan asalin kasar Congo ya isa kasar a jihar Lahadi.Babban aikin da ke wuyansa shi ne taimaka wa hukumomin mulkin soji damar shirya zabuka na dimokuradiyya kamar dai yadda suka alkawarta bayan mutuwar shugaba Idris Deby.

Talla

Manzon na kungiyar Tarayyar Afirka mai shekaru 74 a duniya, kwararren jami’in diflomasiyya ne da ya yi fice a duniya, to sai dai akwai gagarumin aiki da ke jiransa a Chadi, kasa ta farko da kasashen duniya suka gaza kakaba mata takunkumai duk da cewa sojoji sun karbi ragamar mulki ta hanyar da ta saba wa kundin tsarin mulki.

An nada Basile Ikouébé,  kan wannan matsayi ne bayan da gwamnatin mulkin sojin Chadi ta ki amincewa da Ibrahim Fall dan kasar Senegal wadda aka nada kan wannan mukami a cikin watan Yunin da ya gabata.

Babban aikin da ke gabansa bayan fara aiki shi ne, tislata wa majalisar mulkin soji ta CMT mutunta kuduri mai lamba 996 da Kwamitin Tsaro na kungiyar ta AU ya amince da shi, da ke neman sojoji su tabbatar da an shirya zabubuka a cikin watanni.

Har ila yau manzon na kungiyar Tarayyar Afrika, aiki ya rataya a wuyansa don tabbatar da cewa ba daya daga cikin sojoji ko fararar hular da ya rike mukami a gwamnatin rikon kwayar da zai tsaya takarar neman wani mukami a wadannan zabubuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI