Cote d'Ivoire

Ouattara da Gbagbo sun gana karon farko cikin shekaru 10

Alassane Ouattara da Laurent Gbagbo.
Alassane Ouattara da Laurent Gbagbo. AFP - ISSOUF SANOGO

A karon farko bayan shekaru 10, shugaban Ivory Coast Alasane Ouattara ya gana da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo a birnin Abidjan.

Talla

Wannan ganawa ita ce ta farko tun bayan kazamin tarzomar da ta barke tsakanin shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2011.

A lokacin da yake karbar bakuncin tsohon shugaban kasar Laurent Gbaagbo a fadar gwamnati da ke cibiyar kasuwancin kasar Abidjan, shugaba Ouattara ya bayyana farin cikinsa da ziyarar.

Musabbabin tarzomar da aka yi a Ivory Coast, shi ne kin amincewa da shan kaye bayan zaben da aka gudanar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 3.

Bayan da aka tilasta masa barin shugabancin, Gbagbo an tasa keyarsa zuwa kotun kasa-da-kasa, ICC da ke Hague inda aka zarge shi da hannu wajen kisan mutane.

Yanzu haka ya rage ga masu lura da harkokin kasar  don ganin rikicin kasar ya zama tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.