Kamaru-Boko Haram

‘Yan Boko Haram sun kashe sojoji biyar da farar hula daya a Kamaru

Wasu sojojin Kamaru a  Dabanga, arewacin kasar, Yuni 2014.
Wasu sojojin Kamaru a Dabanga, arewacin kasar, Yuni 2014. AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Ma’aikatar tsaron Kamaru ta tabbatar da mutuwar sojojin kasar biyar da kuma farar hula daya, a wani harin da mayakan Boko Haram suka kai a lardin Arewa mai nisa na kasar.

Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron ta fitar a yammacin jiya Talata, ta ce dakarun sun hadu da ajalinsu ne a ranar Litinin, a daidai lokacin da suke aikin kakkabe mayakan na Boko Haram kusa da iyakar kasar da Najeriya.

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu, ma’aikatar tsaron ta ce sojoji uku da farar huda daya sun samu raunuka.

A ranar Asabar da ta gabata, mayakan na Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru 8 a garin Sagme da ke kusa da iyakar kasar da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.