KOTU-RASHAWA

Equatorial Guinee ta tsare sojojin Faransa shida

Teodorin Nguema Obiang Mongue, mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea a Malabo 2013
Teodorin Nguema Obiang Mongue, mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea a Malabo 2013 AFP

Sojojin Faransa 6 ne a yau alhamis 29 ga watan Yulin 2021 kasar Equatoriale Guine ta kama  a filin sauka da tashin jiragen saman birnin Bata, baban birnin tattalin arizikin kasar.An  kama sojojin ne bayan da suka saukar da jirgin Helikoftansu a jiya laraba a filin jirgin domin shan mai, kamar yadda rundunar sojin Faransa da tashar radiyo da talabijin din gwamnatin yar karamar kasar, dake yankin tsakkiyar Afrika ta sanar. 

Talla

Kalonal Pascal Ianni,  kakakin rundunar sojin Faransa ya ce,  sojojiun sun saukar jirgin mai saukar Agulu ne da misalin karfe 2h15 na ranar jiya laraba, sakamakon rashin isashen man fetur, inda yanzu haka suke ci gaba da zaman jiran basu iznin sake cirawa da jirgin nasu.

Har ila yau kakakin rundunar sojin ta faransa ya bayyana cewa, yanzu haka ana  cikin wani yanayi  ne na rashin tabas, inda mahukumtan Guinee ke ci gaba da dakatar da jirgin da kuma sojoji 6 dake cikinsa

A yau alhamis tashar radiyo da talabijin din kasar ta Equatoriale Guine  TVGE, ta ce jirgin , ya sauka ne bayan da samu izni  daga mahukumtan filin jirgin saman.

sojojin 6 dai sun bada bahasi a babbar hedkwatar yan sanda birnin na Bata, inda aka tsare jirgin mai saukar Agulu samfarin Fennec,  da ba ya dauke da makami, na gudanar da  jigilar kayayyaki ne,  tsakanin biranen Douala, cibiyar kasuwancin kasar  Cameroun, da Libreville, babban birnin kasar Gabon, inda Faransa ke da sansanin  soji a wani guri dake kudancin kan iyakar kasar Equatorial Guine.

wanna sabuwar badakala dai, ta biyo bayan ganin a Ranar laraba 28 ga watan na yuli 2021 Kotun kolin Faransa ta tabbatar da hukumcin daurin shekaru 3 kan dan shugaban kasar, haka kuma mataimakin shugaban kasa  Teodoro Nguema Obiang Mangue, da aka fi sani da Teodorin, sakamakon samunsa da laifin zargin karkata kudaden gwamnatin kasarsa ya jibge a kasar ta Faransa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.