Tchadi-Siyasa

Zanga-zangar yan adawa a Ndjamenan Chadi,

Zanga-zangar yan adawa a Ndjamena, Tchadi,  29 juillet 2021.
Zanga-zangar yan adawa a Ndjamena, Tchadi, 29 juillet 2021. © RFI/Madjiasra Nako

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zanga  kan titunan birnin Ndjamenan kasar Chadi a wannan alhamis, domin nuna adawa da gwamnatin mulkin sojin kasar karkashin jagorancin Mahmat Idris Deby, da ya karbi jan ragamar mulkin kasar bayan kashe mahaifinsa Idrisa Deby Etno a fagen daga yau da kimanin kwanaki 100 da suka gabata. 

Talla

Kawancen kungiyoyin fararen hula da na jam’iyyun adawa da ke karkashin jagorancin Succes Masra ne, ya bukaci  gudanar da zanga zangar ta yau, don nuna adawa da abin da ya kira da  kwace mulki da majalisar zartarwar mulkin sojin kasar CMT ta yi karkashin jagorancin Mahmat Idris Deby.

Masu zanga-zangar na bukatar ganin majalisar mulkin sojin ta shirya babban taron mahawarar yan kasa da zata bai wa illahirin bangarorin al’ummar kasar damar tura wakilansu domin tattauna makomar kasar.

A wannan karo dai mahukunta sun bai wa jama’a damar gudanar da zanga-zangar kan wani titi mai tsawon kilomita 3 dake  birnin Ndjamena, duk da cewa an baza dimbin jami’an tsaro domin tsare  muhimman wurare da ke birnin.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar dai, na dauke ne da manyan allunan da aka yi wa rubutun da ke sukar lamirin majalisar mulkin sojin. a yayin da wasu kuwa ke dauke da  rubatun Kalmar dake cewa ‘’Faransa fita daga kasarmu ta Chadi’’, ya yin da wasu fusatatun matasa kuma suka kona tutar Faransa lokacin zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.