Kungiyar MSF ta koka dangane da halin da mata suka samu kan su a Kamaru
Wallafawa ranar:
Akalla mutane kusan dubu 700 suka kauracewa yankunan su a kudu maso yammacin Kamaru,yankin da tabarbarewar lamuran tsaro ke zama cikas ga jama’a wajen amfana da asibitoci duk da kokarin kungiyoyi masu zaman kan su
Matsallar tsaro ta tilastawa duban mazauna yankunan kudu maso yammacin kamaru tserewa daga yankin,inda rahotanni ke dada nuna cewa magidanta da dama ne suka bar ya’a da matan su domin cira da rayukan su.
Mata masu juna biyu na daga cikin wandada ke wahala,dan karamin misali na wannan mata mai dauke da ciki dake da sunan Rosemary da ta share kusan kwana guda ta na tafiya kafin ta samu isowa wani kauyen,inda jama’a suka taimaka tareda gayyato motar daukar marasa lafiya dake aiki da kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF.
Labarin wannan mata na daya daga cikin matsalolli da akasarin mata mazauna wadanan yankuna ke fuskanta yanzu haka musaman yankin kudu maso yammacin kasar ta Kamaru da aka fi sani da yankin masu amfani da harshen ingilishi,yankin da da jimawa kungiyoyi jama’a wasu ta fuskar siyasa,yayinda wasu ke dauke da makamai suka bukaci balewa daga kasar Kamaru.
Rahotanni na dada nuni cewa an cin zarrafin farraren hula,jami’an kiwon lafiya ba su cira ba,hata dalibai na fuskantar muzgunawa musaman lokacin da aka kulle jama’a sabili da cutar Covid 19.
Wasu alkaluma daga majalisar dimkin Duniya,na nuni cewa kusan asibiti daya daga cikin biyar dake yankin ne ya daina aiki sabili da rashin tsaro a wannan yanki da aka tilastawa kusan mutane dubu 700 zama yan gudun hijra.
Tarin wadanan matsalloli na daga cikin abinda ke hana jama’a amfana ko cin moriyar asibitoci a wannan yanki,yayinda binciken karshe ke dada nuni cewa jama’a ba su da karfi biyan kudadde a asibitocin dake karkashin gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu