Dan Ghaddafi ya bayyana aniyar takarar shugaban Libya
Wallafawa ranar:
Saif al-Islam, dan shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi da aka kashe a shekarar 2011 ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar, tare da maido da hadin kanta, bayan yakin da aka shafe shekaru 10 ana yi ya wargaza ta.
Ya bayyana haka ne wata ganawa da ya yi da jaridar ‘New York Times’ a gidansa da ke garin Zintan, yammacin kasar da ke arewacin Afrika.
Dan shekaru 49 din, wanda kafin shekarar 2011 ake mai kallon wanda zai gaji mahaifinsa ya ce a cikin shekaru 10 da suka wuce, babu abin da ‘yan siyasa suka tsinana wa kasar face ukuba da tashin hankali, yana mai cewa lokaci ya yi da za a koma yadda ake a da.
An shafe shekaru ba tare da an san inda al-Islam, wanda kotun hukunta laifukan yaki ke nema ruwa jallo ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu