Jirgin ruwa Ocean Viking ya ceto bakin haure 195 saman tekun Libya
Wallafawa ranar:
Wani jirgin ruwa mai suna Ocean Viking dake aikin ceto yan cin rani a teku ya samu nasarar ceto bakin haure 195 a saman tekun Mediterrane a kan iyaka da gabar ruwan Libya.
Da safiyar jiya asabar an bayyana cewa wannan jirgi yayi nasarar ceto mutane 57 na farko dake cikin wani kwale-kwale saman tekun mediterrane.
Kungiyoyi da dama na ci gaba da fadakar da masu kokarin neman tsallakawa zuwa Turai a wannan lokaci da su kaucewa yin amfani da kananen jirage na ruwa,wandada ke haddasa mutuwar baki da dama.
A cewar hukumar dake sa ido a kan bakin haure a Duniya akalla bakin haure 1.146 ne suka mutu a kokarin su na shiga turai ta teku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu