Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

'Yan tawayen Afirka ta Tsakiya sun kashe fararen hula 6

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kauyen Yade, dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kauyen Yade, dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. © REUTERS

‘Yan tawaye a Afirka ta tsakiya sun hallaka fararen Hula shida tare da jikkata wasu da dama, a wani hari da su ka kai kan wani karamin kauye dake arewa maso gabashin kasar.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan tawayen sun kai harin ne kan sansanin sojoji da ke kauyen Mann, mai nisan kilomita 550 daga babban birnin kasar Bangui.

Majalisar dinkin duniya ta koka bisa yadda ‘yan tawayen kasar suka matsa da kai hare-hare a baya bayan na, kan sassan kasar.

Africa ta tsakiya ita ce kasa ta biyu da jama’arta ke fama da tsananin talauci a duniya, wanda hakan ya faro ne tun lokacin da rikicin ‘yan tawaye ya barke a 2013.

Baya ga wannan kuma kasar ta sha fama da matsalar juyin mulki daga jami’an sojoji tun lokacin da kasar Faransa da ta mulki  ta bata ‘yancin kai a 1960.

Rashin kwanciyar hankalin da kasar ke fama da shi ne ya sanya majalisar dinkin duniya ta aike da dakarun wanzar da zaman lafiya don tabbatar da tsaro a kasar, a yayin da jami’an tsaron Rwanda ke kula da kan iyakokin ta.

Ko a ranar Alhamis din da ta gabata sai da majalisar dinkin duniya ta kara tura dakaru kasar da zasu yi aiki na tsahon watanni 12 duk don magance tashe-tashen hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.