Congo-Hatsari

Hatsarin mota ya kashe mutane 33

Ana yawan samu hatsurran motoci a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, lamarin da ke haddasa asarar daruruwan rayukan al'umma.
Ana yawan samu hatsurran motoci a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, lamarin da ke haddasa asarar daruruwan rayukan al'umma. © africafeeds

Akalla mutane 33 ne suka rasa rayukansu bayan motarsu ta yi taho-mu-gama da wata katuwar tankar dakon man fetur a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a karshen makon nan.

Talla

Fasinjojin sun kone kurmus bayan wuta ta tashi a sanadiyar karon da motocin biyu suka yi a ranar Asabar cikin dare a yankin Kudancin kasar kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sanda, Antoine Pululu ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

A ranar Litinin din nan aka gudanar da jana’izar burbushin gawarwakin mutanen da lamarin ya cika da su.

Mummunan hatsarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Kibuba mai tazarar kilomita 80 daga babban birnin kasar, Kinshasa.

Hadduran ababan hawa na yawan aukuwa a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo sakamakon karababbun motocin da ke mamaye kan titunan kasar, kuma akasarinsu ba su cika  ka’idojin zirga-zirga ba.

Kazalika hanyoyin motocin kasar cike suke da ramuka, sannan da dama daga cikin direbobi na yin tatur da barasa kafin su dau hanya, yayin da wasunsu ba su da kwarewa.

Ko a shekarar 2018, sai da aka samu asarar rayukan mutane 53 a kan hanyar da ta sada Kinshasa da tashar jiragen ruwa ta Matadi a sandiyar hatsarin tankar mai.

Sannan a 2010, akalla mutane 230 ne suka kone kurmus a kasar bayan wata tankar dakon mai ta kife a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.