Coronavirus-Lafiya

Korona ta yi wa Afrika irin kamun da ta yi wa India

Korona ta gigita India a 'yan makwannin da suka gaba, inda ta yi ta lakume dubban rayuka a kowacce rana
Korona ta gigita India a 'yan makwannin da suka gaba, inda ta yi ta lakume dubban rayuka a kowacce rana JUNI KRISWANTO AFP

Shugaban hukumar yaki da yaduwar cututuka a Afirka Dr. John Nkengasong, ya ce halin da ake ciki a nahiyar, ya yi kama da wanda kasar India ta fuskanta, sakamakon yawan mutanen da ke kamuwa da cutar Covid-19, yayin da a hannun daya asibitoci ke fama da karancin kayan aiki.

Talla

"Yanayin da ake ciki a nahiyar na matukar tada hankula saboda a yau akwai akalla mutane miliyan 6 da dubu 500 da suka harbu da wannan cutar a Afirka. A game da zagaye na 3 na wannan cuta kuwa, tuni ta bayyana a cikin kasashe 29, yayin da wasu kasashen biyu wato Algeria da Tunisia suka shiga zagaye na 4 na cutar." inji Dokta Nkengasong.

Doktan ya kara da cewa,

Lura da alkaluman da muke da su a yau, mafi yawan kasashen da mutane suka fi kamuwa da cutar na yankin kudanci da gabashin Afirka ne, amma akwai wasu a yankin arewacin nahiyar da suka hada da Masar da Libya, Mauritaniya har ma da Nijar.

 

"Mafi yawan kasashen Afirka na fama da irin matsalar da kasar India ta fuskanta, asibitoci sun cika da marasa lafiya, ga karancin iskar taimaka wa don numfashi musamman a Zambia da Namiba da Botswana duk suna fama da irin wannan matsala" kamar yadda ya yi karin haske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.