FIFA-DAKATARWA

Fifa ta haramtawa Issa Hayatu shiga harakokin kwallon kafa

Tsohon shugaban Hukumar Kwallon kafar nahiyar Afrika , Issa Hayatou (hagu), a lokacin taron musaman na hukumar kwallon kafa ta duniya  Fifa, a ranar  26 ga watan fabrairun  2016 à Zurich
Tsohon shugaban Hukumar Kwallon kafar nahiyar Afrika , Issa Hayatou (hagu), a lokacin taron musaman na hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, a ranar 26 ga watan fabrairun 2016 à Zurich AFP

Kwamitin da’a na Hukumar kwallon kafa ta duniya ya sanar da dakatar da tsohon shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka Issa Hayatou na shekara guda sakamakon badakalar wani kwangilar kasuwanci da wata kafar talabijin na kasar Faransa da ake kira ‘Lagardere Sports‘ wanda ya sabawa dokokinta.

Talla

Kwamitin ya kuma bukaci Hayatou da ya biya tarra Dala dubu 33 saboda sabawa dokar hukumar mai lamba 15.

Binciken da akayi akan tsohon shugaban hukumar kwallon kafar ya biyo bayan kulla yarjejeniyar kwangilar kasuwanci da kafofin yada labarai dangane da wasannin hukumar tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017.

Kwamitin ya gano cewar Hayatou ya sabawa dokokin aikin sa a matsayin shugaban Hukumar CAF wajen kulla yarjejeniyar wanda ya ya shafi kimar hukumar da kuma ka’idodin ta.

Hukumar CAF ta kulla yarjejeniya da kamfanin Lagardere Sports na kudin da ya kai Dala biliyan guda domin karbe ikon nuna wasannin gasar cin kofin Afirka daga shekarar 2017 zuwa 2028 abinda ya sanya kaddamar da bincike akai.

A shekarar 2017 aka sauke hayatou daga shugabancin CAF bayan ya sha kaye a zaben da suka kara da Ahmad Ahmad daga kasar Madagascar.

Hayatou ya dade yana jagorancin Hukumar CAF da kuma zama mataimakin shugaban Hukumar FIFA abinda ya bashi damar jagorancin ta na wucin gadi tsakanin watan Oktobar shekarar 2015 zuwa Fabarairun shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI