Kamaru-'Yan aware

Human Rights Watch ta zargi kashe fararen hula a Kamaru

wata mota mai sulke ta sojin kasar Kamaru ta na gudanar da sunturin tsaron  à Lysoka, kusa da Buea,
wata mota mai sulke ta sojin kasar Kamaru ta na gudanar da sunturin tsaron à Lysoka, kusa da Buea, MARCO LONGARI / AFP

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta zargi ‘yan aware da kuma dakarun gwamnatin Kamaru da kashe fararen hula a yankin kasar mai amfani da turancin ingilishi na kasar 

Talla

A rahotan da ta fitar, kungiyar ta Human Rights Watch ta ce a Yankin Arewa maso yammacin kasar, an kashe fararen hula biyu tsakanin ranar 8 zuwa 9 ga watan yuni, kuma bincke ya tabbatar da cewa dakarun gwamnati ne suka aikata kisan.

Hakazalika kungiyar ta yi zargin cewa akwai mata da dama da aka yi wa fyade, sai kuma wawashe dukiyoyi a gidaje akalla 30, ciki har da gidan wani basaraken gargajiya duk tsakanin 8 zuwa 9 ga watan na yuni.

Kwanaki biyu kafin haka wato ranar 6 ga watan na yuni, ‘yan aware sun kashe wani yaro dan shekaru 12 a duniya da kuma wani malamin makaranta a Yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Rahoton ya kuma ce an sace mutane 4 a ranar 25 ga watan na yuni, abin da ke tabbatar da cewa ana samu yawaitar aikata laifufuka daga bangarorin biyu wato dakarun gwamnati da kuma ‘yan aware.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta bukaci mahukuntan kasar ta Kamaru, su dauki matakan da suka wajaba don kare fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.