Kungiyar MSF ta janye ma'aikatanta daga wasu yankunan Kamaru

Jami'an kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF
Jami'an kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF Yuri CORTEZ AFP/Archivos

Kungiyar Medecins Sans Frontieres da ke gudanar da ayyukan jinkai ta fannin kiwon lafiya, ta sanar da janye ma’aikantanta daga lardin Arewa maso yammacin kasar Kamaru mai fama da rikici.

Talla

Kimanin watanni 8 da suka gabata ne gwamnatin Kamaru ta sanar da dakatar da ayyukan kungiyar a wannan yanki domin sake bitar ka’idojin da ke bai wa kungiyar damar ci gaba da aiki, inda a jiya talata jagorar tafiyar da kungiyar a lardin Laura Martin ta ce a yanzu dai sun janye baki daya daga Bamenda.

wasu daga cikin likitocin kungiyar ta MSF
wasu daga cikin likitocin kungiyar ta MSF Lionel HEALING, - AFP/File

Janyewar wannan kungiya daga wannan yanki ya kasance wata babbar matsala ga mazauna kauyuka dake amfana da gundumuwar kungiyar ta MSF a fanin kiwon lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI