Shugaban Ghana na fuskantar bore daga kungiyoyi da mutanen kasar
Wallafawa ranar:
Masu hamayya da salon mulkin shugaba Nana Akufo-Ado na kasar Ghana, sun bukaci jama’a su gudanar da zanga-zangar lumana wannan laraba a birnin Accra don samar da gyara dangane da yadda ake tafiyar mulkin kasar a cewarsu.
Wadanda suka tsara zanga-zangar na zargin gwamnatin Akufo-Ado da gazawa a fagen tattalin arziki, yayin da rashawa ke neman dawowa a kasar, kana suka zargin shugaban da saya wa kansa sabon jirgin sama duk da hali na matsi da al’umma ke ciki.
A cewar shugabanin kungiyoyin kare hakokkin jama’a,gwamnatin kasar ta gaza wajen shawo kan wasu matsalloli tareda kaucewa alkawura da suka dau a baya, jama’a na rayuwa cikin kutsi da talauci duk da arzikin da kasar keda shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu