Rwanda

Dakarun Rwanda na Samun nasarar yaki da masu Jihadi a Mozambique

Sojoji dake cikin Tawagar jami'an tsaro Rwanda sama da 1000 ta musamman da aka aika kasar Mozambique domin yakar ta'addanci, 10 ga watan Yuli 2021.
Sojoji dake cikin Tawagar jami'an tsaro Rwanda sama da 1000 ta musamman da aka aika kasar Mozambique domin yakar ta'addanci, 10 ga watan Yuli 2021. AP - Muhizi Olivier

Dakarun Rwanda dake taimakawa kasar Mozambique yakar masu ikirarin jihadi  sun ce kasa da wata daya suna samun nasara wajen fatattakan masu jihadin wadanda suke neman kassara Mozambique.

Talla

A makon jiya sojan Rwanda suka taimaka aka sami nasarar kwato garin Awasse, wani karamin gari wanda masu jihadi suka kwace a bara.

Kakakin Dakarun Rwanda Kanar Ronald Rwivanga ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa suna samun nasarar dannawa da kwace dukkan wurare dake yankin Cabo Delgado daga hannun masu ikirarin jihadi.

Ya fadi cewa sun sami nasara a wurare biyu kuma suna dab da  mamaye Mocinboa da Praia, yankunan da suka dade hannun masu jihadi tun  12 ga watan Agusta na 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.