Burkina Faso

Masu Jihadi a kasar Burkina Faso sun kashe mutane 30

Sojojin kasar Burkina Faso.
Sojojin kasar Burkina Faso. © REUTERS/Luc Gnago

Hukukokin kasar  Burkina Faso sun ce mutane 30 suka gamu da ajalinsu cikin su harda sojoji 15 sakamakon wani kazamin harin da ake zargin 'Yan ta’adda suka kai a kauyukan dake Yankin arewacin kasar.

Talla

Kauyukan dake kusa da iyakan Jamhuriyar Nijar na fuskantar hare-haren 'Yan ta‘adda, domin ko a ranar larabar data gabata fararen hula 11 aka kashe, yayin da aka sace shanu da kuma wasu kaddarori.

Sanarwar ma’aikatar tsaron kasar ta ce an tura Karin jami’an tsaro yankin tare da 'Yan banga, abinda ya kaiga kashe sojoji 15 da Yan Sakai 4, yayin da aka kashe maharan 10.

Ma’aikatar tsaron tace yanzu haka yankin da aka kai harin na karkashin ikon sojojin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.