Sudan ta Kudu - Yaki

Sudan ta Kudu: Ana kukan targade karaya ta samu

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar.
Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar. REUTERS/Jok Solomun

Shugabannin Jam’iyyar SPLM da ke Sudan ta Kudu sun sanar da sauke mataimakin shugaban kasa Riek Machar daga shugabancin ta saboda abinda suka kira rashin kare muradunsu.

Talla

Sauke Machar daga jagorancin Jam’iyyar ya biyo bayan taron kwanaki 3 da Jam’iyyar ta gudanar kamar yadda bangaren sojin ta ya sanar.

An bayyana nada Babban Hafsa a rundunar sojin, Laftanar Janar Simon Gatwech Dual a matsayin shugaban riko sakamakon sauke Machar.

Sai dai masu sharhi na kallon matakin a matsayin wanda ka iya rikidewa zuwa barazana muddin aka sami tsamin dangantaka tsakanin magoya bayan Riek Machar da na Laftanar Janar Simon Gatwech, lamarin da ka iya haifar da barkewar sabon fada a kasar, da yakin basasa ya tagayyara.

Yayin karin bayyani kan halin da ake ciki bayan sauke Machar daga shugabancin jam’iyyarsa, Edmond Yakani wani fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya ce tuni dakarun SPLM suka rabu inda aka samu tsagi biyu tsakanin masu goyan bayan Riek Machar da masu adawa da shi na babban hafsan soji.

A cewar Yakani, ko shakka babu bangaren da babban hafsan sojin ke da runduna mai karfi, saboda yadda kwamandoji soji ke goya masa baya. Saboda haka yanzu Machar na fama da matsala wajen tafiyar da SPLA dangane da bukatar hada kann dakarun dake Sudan ta Kudu.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.