Chadi - Ta'addanci

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Chadi fiye da 20

Sojojin kasar Chadi yayin sintiri a cikin wata kasuwa bayan mutuwar shugaba Idriss Deby a N'Djamena, babban birnin kasar. 26 ga Afrilu, 2021.
Sojojin kasar Chadi yayin sintiri a cikin wata kasuwa bayan mutuwar shugaba Idriss Deby a N'Djamena, babban birnin kasar. 26 ga Afrilu, 2021. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA

Rahotanni daga Chadi sun ce an kashe sojojin kasar 24 tare da jikkata wasu da dama a ranar Laraba, yayin wani hari da ake zargin mayakan ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ne suka kai a yankin Tafkin Chadi mai fama da tashin hankali.

Talla

Bayanai sun ce sojojin da mayakan Boko Haram suka kaiwa farmakin na tsaka da hutawa ne bayan dawowa daga sintiri a ranar Laraba, kamar yadda mataimakin shugaban yankin, Haki Djiddi, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Djiddi ya ce sojoji 24 ne suka mutu, yayin da kuma da dama suka jikkata, wasu kuma suka watse cikin karkara.

Mai magana da yawun rundunar sojin Chadi Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce an kai harin ne a Tchoukou Telia, tsibiri mai nisan kilomita 190 a arewa maso yamma da N'Djamena babban birnin kasar, said ai bai bayyana adadin dakarun da suka mutu ba.

Mayakan Boko Haram sun dade suna amfani da yankin Tafkin Chadi tsawon shekaru a matsayin mafaka inda suke kai hari kan sojoji da fararen hula a yankunan Najeriya, Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Ko a cikin watan Maris na shekarar 2020, kusan sojojin Chadi 100 aka kashe a wani farmakin cikin dare a tsibirin Bohoma, abinda ya sanya tsohon shugaban kasar at Chadi marigayi Idris Deby Itno kaddamar da gagarumin farmaki kan Boko Haram, wanda daga bisani yayi ikirarin kashe mayakan kungiyar fiye da dubu 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI