JUYIN-MULKI

Sojoji sun yi shelar juyin mulki a Guinea

Tababa da rashin tabbas sun mamaye fagen siyasar Guinea samakon ikrarin sojin kasar cewar sun gudanar da juyin mulki sun kuma kama shugaba kasa Alpha Conde, yayin a bangare guda gwamnati ke cewa ta murkushe yunkurin.

Shugaba Alpha Conde
Shugaba Alpha Conde © AFP - Michael Tewelde
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace ya samu faifan bidiyo mai dauke da wani hafsan soji kewaye da wasu sojojin dake dauke da bindigogi da yake sanar da kama shugaban kasa da kuma soke kundin tsarin mulkin kasar.

Hafsan sojin ya kuma sanar da rufe iyakokin sama da kasa da kuma rusa gwamnatin kasar, amma kuma gwamnatin Conde ta sanar da gabatar da sanarwar dake bayyana murkushe yunkurin da sojojin suka kai fadar shugaban kasa.

Rahotanni daga birnin Conakry sun tabbatar da jin karar harbe harbe da muggan makamai a kusa da fadar shugaban kasar dake Yankin Kaloum, yayin da mazauna yankin suka ce sojoji sun bukace su da su koma cikin gidajen su.

Wani shaidar gani da ido yace ya ga tawagar sojojin kasar cikin motoci suna tafiya tsakiyar birnin Conakry cikin farin ciki, inda suke harbi sama suka kuma rera wakar soji.

Wani jami’in difloamsiyar yammacin duniya da ya nemi a sakaya sunan sa yace babu tantama harbe harben alamun juyin mulki ne.

Jami’in yace rikicin ya fara ne lokacin da gwamnati tayi yunkurin korar wani kwamandan zaratan sojin kasar, abinda ya tunzira sojojin suka mamaye fadar shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa bai iya tantance wannan matsayi ba, amma wannan ba wani sabon abu bane a kasar Guinea inda ko a shekarar da ta gabata sojoji sun yi irin wannan yunkurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI