HARIN-TA'ADDANCI

'Yan ta'adda sun kashe mutane 480 a Burkina Faso

Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore © REUTERS/Fabrizio Bensch/File Photo

Kungiyar agaji ta kasar Norway tace ‘Yan bindigar dake ikrarin jihadi a Burkina Faso sun hallaka mutane akalla 480 tsakanin watan Mayu zuwa Agustan wannan shekara.

Talla

Kungiyar agajin ta bayyana damuwa dangane da karuwar yawan mutanen dake mutuwa da kuma rasa matsugunan su a watannin da suka gabata, ganin yadda aka tilastawa mutane sama da dubu 275 tserewa daga matsugunan su domin tsira da rayukan su tun daga watan Afrilun da ya gabata.

Alkaluman kungiyar sun nuna cewar akalla mutane dubu 55 ake rabuwa da matsugunan su kowanne wata, abinda ke nuna yadda adadin ya ninka har sau 3 sabanin yadda aka gani tsakanin watan Oktobar shekarar 2020 zuwa Maris din shekarar 2021.

Rahotan kungiyar yace alkaluman ta ya nuna cewar mutane sama da miliyan guda da dubu 400 suka tsere daga gidajen su domin kaucewa hare haren.

Kungiyar tace tsaikon da ake samu wajen kaiwa jama’a dauki domin basu kayan jinkai na tilastawa mutane zabi tsakanin matsalar tsaro da kuma yunwa.

Rahotan kungiyar yace wannan ya sa wasu mutane zabin ci gaba da zama a yankunan da ‘Yan bindigar suka mamaye, duk da karancin abincin da suke fuskanta, abinda ke kaiga wasu cin ganyen itatuwa domin kare lafiyar su.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Burkina Faso da ta bata izinin shiga yankunan domin taimakawa jama’ar dake fuskantar wannan matsala.

Daraktan kungiyar a Burkina Faso, Manenji Mangundu yace kungiyoyin agaji na da karfin taimakawa jama’ar dake cikin yankunan da zuwa gare su ke tattare da hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.