AFIRKA-KORONA

Afirka ta gaji da jiran taimakon maganin rigakafin korona - AU

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus AP - Balazs Mohai

Kungiyar kasashen Afirka ta AU tace ta bayyana shirin sayen maganin rigakafin cutar korona domin rabawa kasashen dake nahiyar, maimakon jiran taimako daga kasashen duniya.

Talla

Jakadan Kungiyar na musamman Strive Masiyiwa ya ce taimakon da ake baiwa kasashen nada kyau, amma ya dace su sayi na su domin yiwa jama’ar su rigakafin maimakon jiran agaji daga wasu nahiyoyi.

Masiyiwa ya bukaci kamfanonin dake sarrafa maganin da su cire dokar hana safarar maganin domin baiwa Afirka damar samun sa, ganin yadda yankin ke ci gaba da fuskantar matsala saboda yadda kasashe masu arziki suka saye magungunan da ake sarrafawa.

Maganin rigakafi samfurin Moderna
Maganin rigakafi samfurin Moderna Jacob King POOL/AFP/Archivos

Jakadan yace masu sarrafa maganin na da hakkin daidata yadda ake raba shi domin ganin kowanne bangare ya samu, sabanin yadda akeyi yanzu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace akalla mutane 9 suka samu maganin daga cikin ko wadanne mutane 100 dake Afirka, abinda ke nuna yadda sauran yankunan duniya suka yiwa Afirka fintinkau wajen yiwa jama’ar su rigakafin.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya tabbatar da wannan matsalar, wanda yace tana matukar damun su.

Gebreyesus yace dogon lokacin da ake samu wajen wadata kowanne bangaren duniya da maganin rigakafin zai bada damar ci gaba da yada cutar da kuma yiwa tattalin arzikin duniya illa.

Daraktan yaki da cututtuka na Afirka John Nkengasong yace kashi 3 da rabi ne kawai na jama’ar Afirka suka karbi allurar rigakafin, yayin da Hukumar Lafiya ke fatar ganin kashi 40 na jama’ar kowacce kasa sun samu rigakafin nan da karshen wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.