Kamaru - 'Yan aware

'Yan awaren Ambazonia sun kashe sojojin Kamaru 9

Dakarun Kamru yayin wani sintiri a yankin Amchide, arewacin kasar.
Dakarun Kamru yayin wani sintiri a yankin Amchide, arewacin kasar. AFP

Rohatanni daga kasar Kamaru na cewa akalla sojojin kasar 9 suka gamu da ajalinsu sakamakon hare-hare maban-banta da mayakan ‘yan aware dake neman ballewa don kafa jamhuriyar Ambazonia suka kaddamar a yankin arewa maso yammaci da ake amfani da turancin Ingilishi.

Talla

Kafofin yada labaran kasar Kamaru sun ruwaito cewa, hare-haren farko da mayakan ‘yan awaren suka kai wasu sansanonin soji uku a Nkambe, Noni da Ndu a yankin Arewa maso Yamma ranar Lahadi ya hallaka sojoji 7.

Yayin da a ranar Asabar wani harin kwantar bauna ya hallaka sojoji 2 a Chouame duk cikin yankin na arewa maso yamma da ake amfani da turancin Ingilishi.

Ya zuwa yanzu rundar sojin Kamaru bata ce uffan ba, dangane da hare-haren na karshen mako a yankin da ta dauki kusan shekaru 4 tana fafatawa da ‘yan aware masu dauke da makamai dake neman ballewa domin kafa kasar Ambazonia, wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan sama da mutane 3500 ciki har da jami’an tsaro dubu 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.