Guinea

Jagoran juyin mulkin Guinea ya ce ba zai tsaya takara ba

Kanar Mamady Doumbouya, a yayin karbar rantsuwar kama aikia. matsayin shugaban gwamnatin riko na Guinea.
Kanar Mamady Doumbouya, a yayin karbar rantsuwar kama aikia. matsayin shugaban gwamnatin riko na Guinea. © CELLOU BINANI/AFP

Jagoran juyin mulkin soji na Guinea, Kanar  Mamady Doumbouya, ya ce ba zai tsaya takara a yayin zaben kasar ba. 

Talla

Jagoran sojojin na Guinea ya bayyana haka ne jim kadan bayan da a ranar Juma’a aka rantsar da shi a matsayin shugaban rikon kwaryar gwamnatin sojojin kasar da suka kawo karshen mulkin tsohon shugaba Alpha Conde. 

Doumbouya, wanda shugaban kotun kolin kasar Mamadou Sylla ya erantsar da shi, ya yi alkawarin cewa daga shi har abokansa da suka yi juyin mulkin kasar babu wanda zai yi takara a zaben da za su shirya.

Ko a ranar Ltinin da ta gabata, sai da majalisar mulkin sojin kasar ta Guinea ta fitar da wata sanarwar a game da haramta wa jami’anta tsayawa takara a zabukan kasa da na kanana hukumomi da za a shirya nan gaba.

A cikin makonni 2 da suka wuce, sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi ta ganawa da manyan ‘yan kasuwa da masu fada a ji a kasar, a game da tsara jadawalin mika mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI