Habasha

An rantsar da Abiy Ahmed na Habasha a sabon wa'adinsa

Firaministan Habasha  Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed EDUARDO SOTERAS AFP/File

An rantsar da Firaministan Habasha Abiy Ahmed domin fara sabon wa’adin shekaru biyar kan karagar mulkin a daidai lokacin da yankin arewacin kasar ke fama da yake-yake.

Talla

A cikin watan Yunin da ya gabata ne,  jam’iyyar Abiy ta Prosperity Party ta samu gagarumar nasara  a zaben da aka gudanar, nasarar da hukumomin gwamnatin tarayyar kasar suka bayyana a matsayin sakamakon sauyin da Firaministan ya kawo a 2018, lokacin da ya fara hawa kujerarsa.

Sai dai nasarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da dubban mutane suka rasa rayukansu a yankin Tigray da ke arewacin kasar, yayin da wasu dubban suka tsunduma cikin bala’in yunwa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, lamarin da ya rage kimar Abiy wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a idon duniya.

Tashin hankalin da ya barke a Tigray ya yadu har zuwa garuruwan Afar da Amhara masu makwabtaka.

Kawo yanzu dai ba a fayyace  kan ko rantsuwar da Abiy ya shafa a yau Litinin za ta sauya matsayar gwamnatinsa ta girke dakaru masu yaki da Kungiyar TPLF wadda ta mamaye karfin fa-aji a yankin na Tigray.

Ofishin Abiy dai ya bayyana cewa, zai dauki matakan ssasantawa da ‘yan tawayen Tigray ne bayan an kafa sabuwar gwamnati a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI