Mali-Faransa

Mali ta yi sammacin jakadan Faransa kan kalaman Macron

Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga.
Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga. © AFP/Annie Risemberg

Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta ce kasar ta gayyaci jakadan Faransa a Bamako, biyo bayan sukar da Shugaba Emmanuel Macron ya yiwa salon mulkin kasar dama kokarinta na yaki da hare-haren ta'addanci a kasar ta yankin Sahel.

Talla

Wata sanarwar ma’aikatar wajen Malin da ke tabbatar da sammacin jakadan na Faransa, ta ce Mali na bukatar karin bayani dangane da caccakar Emmanuel Macron kan salon kamun ludayin gwamnatin ta Bamako dama kokarinta na magance matsalolin tsaron da suka dabaibaye kasar.

Cikin kalaman na Macron a jiya talata ya bukaci Sojin na Mali su mayar da hankali wajen kwato yankunan da ke karkashin ikon mayaka masu ikirarin jihadi, kalaman na gwamnatin ta Mali ke kallo a matsayin shagube.

Dangantaka ta fara tsami tsakanin Malin da kasar ta Faransa da ke matsayin uwar goyonta da ta yi mata mulkin mallaka, tun bayan janye wani kaso na sojojin da ke taimakawa kasar a yaki da ayyukan ta’addanci a bangare guda kuma Malin ta fara tattaunawa da kamfanin Wagner na Rasha don daukar Sojin hayar da za su tayata yaki da ta'addanci.

Kazalika kalaman Firaminista Choguel Kokalla Maiga gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin Faransar da janyewa daga Mali dai dai lokacin da kasar kef ama da matsalar tsaro, ya fusata shugaba Macron.

Kwana guda bayan ikirarin na Maiga ne kuma Macron ya musanta batun da cewa Faransar ba ta da shirin juya baya ga Malin.

Sammacin Jakadan na Faransa dai ya biyo bayan kalaman Macron a jiya da ke kira ga Malin da cewa ta mayar da hankali a yankunan da ke fama da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI