Mali - Ta'addanci

Sojojin Mali 16 sun mutu a harin mayaka masu ikirarin jihadi

Wasu Sojin Mali a Tumbuktu.
Wasu Sojin Mali a Tumbuktu. AFP - MAIMOUNA MORO

Hukumomi a Mali sun tabbatar da mutuwar sojojin kasar 16 baya ga raunatar wasu 10 bayan da motar tawagar Sojin ta taka nakiyar gefen hanya a yankin tsakiyar kasar mai fama da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da kuma 'yan bindiga a gefe guda.

Talla

Sanarwar da ma'aikatar sojin ta Mali ta fitar, ta ce, bayan da motar ta taka nakiyar, 'yan bindigar da suka dasa ta sun kuma budewa motar sojojin wuta, abinda ya kai ga musayar wuta da kuma kashe tarin muatne tsakanin bangarorin biyu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sojin a bangarensu sun hallaka maharan 5 yayin musayar wutar.

Kasar Mali na ci gaba da fama da matsalar mayaka masu ikirarin jihadi da kuma 'yan bindiga tun bayan barkewar rikicin shekarar 2012, bayan da masu ikirarin jihadin suka yi yunkurin kwace iko da mulkin kasar.

Rikicin na Mali zuwa yanzu ya hallaka mutane fiye da dubu 500 baya ga tilasta miliyoyi kaura daga yankunansu don tsira da rayukansu.

Ka zalika yanzu haka wasu sassa na kasar ta Mali na karkashin ikon mayaka masu ikirarin jihadi musamman daga gabashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI