Kotun Kenya ta ki amincewa da hurumin MDD dangane da rikicin kasar da Somaliya

Babbar kotun daukaka kara ta kasar Kenya
Babbar kotun daukaka kara ta kasar Kenya Simon MAINA AFP/File

Kenya ta ki amincewa da hurumin Kotun Majalisar Dinkin Duniya (ICJ), dake shirin yanke hukunci a mako mai zuwa kan takaddamar iyakokin teku da ta dade tana yi da Somaliya

Talla

Kasashen biyu makwabta dake yankin Kahon Afirka sun shafe shekaru suna takaddama a kan tekun Indiya da da kowannen su ke ikirarin mallakar yankin mai man fetur da kuma iskar gas.

Wasu yan kasar Kenya
Wasu yan kasar Kenya © SHOFCO

Tun a watan Maris Kenya ta sanar da shirin kauracewa zaman kotun ICJ a shari’ar da tuni kotun da ke Hague ta ki amincewa da bukatar dage ta, inda ake saran zartar da hukunci a ranar Talata mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI