Somalia-Ta'addanci

AU za ta fadada aikinta a Somalia don murkushe ayyukan ta'addanci

Wani bangare na dakarun AMISOM dubu 20 da ke aikin yaki da ta'addanci a Somalia.
Wani bangare na dakarun AMISOM dubu 20 da ke aikin yaki da ta'addanci a Somalia. Tina SMOLE AFP/File

Kungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da shirin fadada ayyukan sojinta a Somalia don kakkabe duk wata kungiya da ke alaka da Al-Qaeda dai dai lokacin da wa’adinta na farko a yakar kungiyar ta’addanci ke shirin karewa a ranar 31 ga watan Disamba.

Talla

A baya-bayan nan hare-hare kungiyoyi masu alaka da Al-Qaeda na ci gaba da tsananta a sassan Somalia duk da dakarun AU dubu 20 da ke taimakawa tsaron kasar dai dai lokacin da kasar ke fama da matsalolin siyasa dana tattalin arziki.

Kungiyar ta AU ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya duba yiwuwar kara aikin rundunar ANISOM wanda ke dauke da sojoji dubu 20 a cikin kasar ta Somalia.

Tashe-tashen hankulan da kasar Somalia ta jima ta na fama da shi, ya yi sanadin baiwa kungiyar ta'addanci ta Al Shebaab damar samun gindin zama tare da cin karenta babu babbaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI