Mali-Faransa

Faransa ta fara janye dakarunta daga garin kidal na Mali

Wasu dakarun Barkhane da ke ficewa daga garin Kidan na arewacin Mali.
Wasu dakarun Barkhane da ke ficewa daga garin Kidan na arewacin Mali. AFP

Faransa ta fara janye dakarunta na Barkhane daga garin Kidal da ke arewacin kasar, tare da mika sansanoninsu ga dakarun Majalisar Dinkin Duniya wato Minusma wadanda za su yi aiki kafada-da-kafada da sojojin kasar ta Mali.

Talla

Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa kanar Pascal Ianni, ya ce ayarin farko na dakarun kasar ya bar sansanin da ke birnin Kidal ne da misalin karfe 5 na safiyar talata zuwa wani sabon sansani da ke yankin Gao a arewacin kasar ta Mali.

Tun cikin watan yunin da ya gabata ne Faransa ta sanar da shirin fara janye wasu daga cikin dakarunta daga Kidal, Tumbuktu da kuma Tissalit, matakin da ke tabbatar da alkawarin da shugaba Emmanuel Macron ya yi na rage yawan dakarun sama da dubu 5 zuwa dubu 2 da 500 ko kuma dubu 3 kafin shekara ta 2023.

Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa ya ce za a kammala aikin janye dakarun ne a cikin kwanaki 10 masu zuwa.

Rage yawan dakarun a daidai lokacin da Mali ke fama da matsalar tsaro, mataki ne da ya yi matukar fusata mahukuntan birnin Bamako, inda Firaminista Choguel Maiga ya zargi Faransa da yin gaban kanta wajen daukar wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI