Sudan

Sudan ta sanya haramcin bulaguro kan wasu mukarraban gwamnati 11

Firaminsitan Sudan Abdallah Hamdok.
Firaminsitan Sudan Abdallah Hamdok. ASHRAF SHAZLY AFP

Ma’aikatar tsaron Sudan ta sanya dokar hana tafiye tafiye kan mambobin kwamitin da ke sanya idanu wajen mayar da kasar kan turbar demokradiyya dai dai lokacin da rikici ke sake tsananta tsakanin bangaren fararen hula dana sojojin da ke mulkin kasar a yanzu tun bayan yunkurin juyin mulkin makwannin baya da bai yi nasara ba.

Talla

A ranar 21 ga watan Satumban da ya gabata ne Firaminista Abdallah Hamdok ya bayyana yadda wasu sojoji da ke biyayya ga hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir suka nufaci kwace iko da mulkin kasar.

Wasu majiyoyi sun ce haramcin tafiye-tafiyen ya shafi mutane 11 galibinsu mambobin da ke cikin kwamitin warware manufofin tsohon shugaban kasar al-Bashir, tare da kokarin mayar da kasar turbar demokradiyya.

Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani daga kwamitin ko gwamnatin kasar dangane da dalilin haramcin tafiye-tafiyen, sai dai a baya-bayan nan ana fuskantar takun saka tsakanin bangarorin da ke tafiyar da gwamnatin kasar.

Bayanai sun ce cikin wadanda haramcin tafiye-tafiyen ya shafa har da Mohamed al-Faki wanda ya zargi Sojojin da ke mulki a kasar da fakewa da zargin yunkurin juyin mulki don samun damar ci gaba da kasancewa a madafun iko.

Majiyar da ke zayyano sunayen wadanda haramcin ya shafa ta sanyo sunan Salah Manaa wanda tuni ya bar kasar zuwa birnin Alqahira na Masar.

Masana dai na kallon haramcin tafiye-tafiyen kan mutane 11 baya kan ka’ida la’akari da yadda ya fito daga wani kwamitin tsaro na musamman maimakon Ofishin babban mai shigar da kara na gwamnati da aka saba gani bisa tsarin doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI