Kamaru-'Yan aware

Hankula sun tashi a Kamaru bayan dan sanda ya kashe daliba a Ambazonia

Yankin masu amfani da Turancin Ingilishi da ke fama da rikici a Kamaru.
Yankin masu amfani da Turancin Ingilishi da ke fama da rikici a Kamaru. © AFP

Mahukuntan Kamaru sun bukaci kwantar da hankula a yankin yammacin kasar mai amfani da turancin Ingilishi bayan kisan da jami’in dan sanda ya yiwa wata yarinya dalibar makaranta.

Talla

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a yankin Buea inda ake ci gaba da fuskantar rikici tsakanin ‘yan aware da kuma dakarun gwamnatin Kamaru tsawon shekaru 4.

A jawabinsa ta gidan talabijin din CRTV gwamnan yankin kudu maso yamma Bernard Okalia Bilai ya ce tabbas lamarin abin takaici ne amma akwai bukatar kwantar da hankula.

Gwamna Bilai ya sha alwashin tabbatar da adalci kan yadda dan sanda ya yi amfani da karfin kakinsa wajen kisan yarinyar karama.

Shugaban wata karamar kungiya da ke rajin kare hakkin dan adam a kasar ta Kamaru Blaise Chamango ya ce jami’in dan sandan ya yi kokarin tsayar da wata mata ne a shingen bincike lokacin da ta ke tuka yara zuwa makaranta a mota inda matar taki tsayawa dalilin da ya sanya jami’in bude wuta.

Bayanai sun ce a tashin farko yarinyar ta samu raunuka amma bayan kai ta asibiti rai ya yi halinsa.

Fiye mutane 500 ne suka yi tattaki zuwa Ofishin gwamnan yankin dauke da gawar yarinyar suna masu neman tabbatar da adalci kan kisan da aka yi mata ba tare da hakki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI