Amurka

Janet Jackson ta yi haifuwar farko tana shekaru 50

Janet Jackson mawakiyar Amurka
Janet Jackson mawakiyar Amurka REUTERS/Kevork Djansezian/File Photo

Fitacciyar mawakiyar Amurka Janet Jackson ta sanar da samun karuwar da namiji a haifuwarta ta farko tana shekaru 50 a duniya.

Talla

Jackson da mijinta Wissam Al Mana balarabe kuma hamshakin attaijiri a kasar Qatar sun rada wa jaririn sunan Eissa.

Janet Jackson kanwa ga marigayi Michael Jackson ta haifu ne ba tare da wani dashe ba duk da tana da yawan shekaru.

Hotunan mawakiyar dai sun ja hankali a lokacin da tana dauke da ciki inda ta yi shiga kamar ta musulmi.

A shekarar 2012 ta auri Al Mana amma ba tare da sanar da duniya ba.

Wakokin Janet sun yi fice musamman a wajajen 1980.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.