Bikin Ba Da Sanda Ga Sabon Lamidon Adamawa

Sauti 20:04

Ranar Asabar 19 ga watan Yuni, shekara ta 2010, gwamnan jihar Adamawa a tarayyar Nigeria Admiral Murtala Nyako GCON, Sarkin yamman Adamawa, ya jagorancin bikin ba da sanda ga sabon Lamidon Adamawa na 12; Alhaji Dr. Muhd. Barkindo Aliyu Mustapha. Mataimakin shugaban tarayyar Nigeria Arc. Namadi Namadi Sambo, da Mai alfarma Sarkin musulmi Dr. Muhd. Sa’ad Abubakar na uku mni, tare da kusan daukacin sarakuna daga dukkan sassan kasar sun albarkaci taron.