Al'adun Gargajiya

Matsalolin rayuwar Bahaushe a gidansa

Sauti

Asali dai ko wace irin al’umma tana da irin al’adarta, don haka bahaushe ma yana da ta shi tsarin al’adar wacce ya gada daga iyaye da kakanni. To sai dai kuma ko wacce al’ada takan ci karo da wasu al’adu ko dabi’u na wasu al’ummu ko dai ta hanyar cudanya ko kuma ta hanyar zamani da kan iya gurgunta al’adar.Al’adar bahaushe ma dai bata tsira ba na cin karo da wasu al’adun da suka haifar da samar da wasu dabi’u da suka sabawa al’adar.A cikin shirin zamu yi nazari ne kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar bahaushe a gidansa.To domin tattauna wannan batu, Shirin Al’adunmu Na Gado yana tare ne da Mallam Ja’afar Shu’aibu wani magidanci da kuma Uwar gida Malama Maimunatu dukkaninsu a Obalande Jahar Legas a Tarayyar Najeriya.