Bahaushen Ba’indiye a Kano Nigeria

Sauti 20:22

Shirin kade kaden karshen mako na gidan rediyon faransa ya tattauna ne da Nazir Abdullahi Magoga wanda ake kira bakin ba’indiye, wanda Allah ya ba shi basirar lakantar harshen Indiyanci ba tare da ya taba zuwa indiya ba. Shirin ya leka duniyar wakokin indiya ne tare da Nazir wanda kuma ya yi sharhi akan wakokin ga masu saurare.Haka kuma a wani shirin na kade kaden karshen mako, Mallam Nazir ya bamu takaitaccen tarihin rayuwarsa tare da wakokinsa wadanda ya sauya daga indiyanci zuwa wakokin yabon Annabi.