Al'adun Gargajiya

Al'adar Aski cikin Wankan Sarautar 'Yan Bori

Sauti 10:05
Le Niger.
Le Niger. L. Mouaoued/RFI

Ranar 2 ga watan daya na shekarar 2011 ne, 'Yan bori suka yi bikin wasan Aski: wankan sarautar Hajiya Rabi Abdu da ta gaji sarautar bori daga mahaifiyarta Hajiya Hajara Ibrahim da aka fi sani da 'Yar Na Bala Sarauniyar 'Yan bori Hausawa mazamna birnin Niamey. Na yi hira da Tsohuwar Sarauniyar wadda ta fayyace ma'ana da kuma yadda ake wannan al'ada ta Aski musamman ma a cikin al'adar Bori. A lokacin al'adar ta Aski Fadawan Sabuwar sarauniyar sun hau bori yayin da masu goge suka rika goge suna jinjina wa aljannun da kowa da takensa.