Al'adun Gargajiya

Al'adar Sauraren Radiyo a Kasashen Hausa

Sauti 10:04

Wata al'adar da aka dade ana dangantawa da rayuwar Bahaushe, itace ta muamala da sauraren Radiyo. A matsayin abokin aiki da nishadi, Radiyo kan kasance zabi mafi sauki wajen samun bayanai a kasashen Hausa. Birni da kauye, kasuwanni,shaguna, kan tituna dama rugagen fulani, babu abokin tarayyan daya dara Radiyo. Kamar yadda bincike ya nuna karancin ilimin boko a arewacin Nigeria da wasu kasashen Hausa,,ilimin da yawancin jaridu da mujallu ke amfani dashi,na cikin wasu dalilan da yasa aka fi muamala da Radiyo a kasashen Hausa. Wasu kan saurari Radiyo domin nishadi,wasu domin karuwa da bayanai,wasu kuma domin dauke wata kewa ko kadaichi. Shirin Duniyar Mu A Yau na wannan mako,ya duba muhimmancin Radiyo ga rayuwar Bahaushe da kuma tasirin wannan muamalar wajen inganta rayuwar Hausawa baki daya.